Miliyoyin mutane a Spain, Iceland da Greenland na shirin kallon wani gagarumin kusufin rana a ranar Laraba 12 ga Agusta 2026, yayin da wata zai rufe rana gaba ɗaya na ɗan lokaci.
Wannan lamari na faruwa ne lokacin da wata zai shiga tsakanin duniya da rana, ya hana hasken rana isa ga wasu sassan duniya.
A wuraren da za a samu cikakken kusufin, za a ga rana ta ɓace gaba ɗaya na ɗan lokaci, lamarin da zai sa sararin sama ya yi duhu kamar dare.
A tsakiyar tekun Atlantika ta Arewa, tsakanin Greenland da Iceland, cikakken kusufin zai kai kusan minti biyu da daƙiƙa 18, wanda shi ne mafi tsawon lokacin da za a iya ganinsa a wannan kusufin.
A Spain kuwa, ana sa ran kusufin zai kasance kusa da lokacin faɗuwar rana, kuma wasu wurare za su samu kusan minti ɗaya da daƙiƙa 50 na cikakken kusufin.
Wannan zai kasance wani lamari na musamman ga Spain, saboda ba a taɓa ganin cikakken kusufin rana a babban yankin ƙasar ba sama da shekara 100.
Wasu ƙasashen Turai ma za su ga wani ɓangare na kusufin. A Madrid, sama da kashi 90 cikin 100 na rana na iya kasancewa a rufe, yayin da Lisbon za ta iya ganin kusan kashi 70 zuwa 80 cikin 100.
A London kuwa, kusan kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na rana ne zai kasance a rufe, yayin da Paris za ta iya samun kusan kashi 45 zuwa 55 cikin 100.
Sassan Greenland za su samu cikakken kusufin, yayin da wasu yankunan Canada da Amurka za su ga wani ɓangare na kusufin.
Masana sararin samaniya sun kuma ce kusufin zai zo daidai da lokacin da Perseid meteor shower ke kololuwa, wanda ke nufin akwai yiwuwar aga wasu taurari masu wutsiya na ratsa sararin sama lokacin cikakken kusufin.
Wannan kusufin rana na 2026 zai biyo bayan wani kusufin wata a ranakun 27 zuwa 28 ga Agusta.
