
Aminu Abdullahi Ibrahim
An ƙaddamar da wani shiri mai suna People, Influence and Action — PIA, da nufin ƙarfafa shigar jama’a da ƙungiyoyin fararen hula cikin harkokin mulki da yanke shawara a Jihar Kano.
An ƙaddamar da shirin ne a wani taron da aka gudanar a Cibiyar Nazarin Dimokuraɗiyya ta Aminu Kano, wato Mambayya, da ke Gwammaja, a nan Kano.
Taron ya haɗa wakilan gwamnati da hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, wakilan al’umma da sauran masu ruwa da tsaki, domin tattauna yadda za a inganta haɗin gwiwa da kuma bai wa jama’a damar shiga cikin harkokin mulki.

Mataimakiyar Daraktar hukumar wayar da kan Jama’a ta Ƙasa, NOA, reshen Kano, Comrade Grace Musa, ta jaddada muhimmancin inganta sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ta ce ingantaccen tsarin karɓar ra’ayin jama’a zai taimaka wajen fahimtar manufofin gwamnati, tare da bai wa hukumomi damar sanin bukatu da ƙorafe-ƙorafen jama’a.
Ta kuma ce shirin Seven for Seven na NOA na daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen ƙarfafa ɗaukar gudanar da aiyuka tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa.

Shi ma mai magana a madadin shirin PIA, Mista Simeon Olatunde, ya ce manufar shirin ita ce sauya jama’a daga kasancewa masu bayyana damuwa kawai zuwa masu shiga cikin matakan neman mafita da kuma yin tasiri a kan manufofin da suka shafi al’ummominsu.
Ya ce shirin zai ƙarfafa ƙwarewar jama’a da ƙungiyoyin fararen hula wajen gano matsalolin mulki, tuntuɓar hukumomin da abin ya shafa da kuma neman mafita da ta dace da bukatun al’umma.
