Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar Manyan Likitocin Dabbobi Ta Nuna Fushinta Kan Kashe Wasu Kananan Giwaye...

Kungiyar Manyan Likitocin Dabbobi Ta Nuna Fushinta Kan Kashe Wasu Kananan Giwaye A Jihar Borno

Date:

Kungiyar manyan likitocin dabbobi ta kasa, ta yi All… wadai da kashe wasu kananan giwaye da aka yi a karamar hukumar Kala Balge dake jihar Borno.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa Dr. Moses Akoroyo ya fitar a Abuja, ta ce abin takaici ne yadda aka nuna wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta na yadda wasu jami’an soji suka hallaka giwayen.

Moses ya ce kungiyar tana sanar da mambobinta da hukumomin kula da gandun daji cewa suna sane da wannan labarin.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda aka kashe wasu shaho guda biyu a yankin jihohin Kebbi da Sakwwato wadanda suka yi hijira daga yankin Turai.

Kazalika shugaban kungiyar, ya ce za su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile wannan al’amari na kashe dabbobin daji dake neman zama ruwan dare.

Latest stories

Related stories