Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoJam’iyyar APC Ta Zargi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Da Tauye Hakkin...

Jam’iyyar APC Ta Zargi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Da Tauye Hakkin Kananan Hukumomin Jihar

Date:

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta zargi gwamnatin NNPP karkashin jagorancin gwamna Abba Yusuf da shirin karkatar da kudaden kananan hukumomi da suka haura Naira miliyan dubu 8.

Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, wanda ya yi wannan zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce gwamnatin NNPP ta kwace mulkin kananan hukumomi, saboda rashin tabbas na siyasa sakamakon tsoron hukuncin da kotun koli za ta yanke kan zaben gwamnan jihar Kano.

Ya ce Jam’iyyar APC a Kano ta samu kwafin takardar amincewa daga ma’aikatar kananan hukumomi inda ta umurci kananan hukumomi 44 da su fitar da kudi sama da Naira biliyan 3 domin gina gadar sama ta Dan Agundi da Tal’udu.

Abdullahi Abbas ya kara da cewa, takardar amincewar wadda ake zargin an aikewa da dukkan shugabannin kansiloli da kuma kwafi ga babban mai binciken kudi na jiha, da na kananan hukumomi ta umurci kananan hukumomin da su bayar da tasu gudummuwar a ayyukan.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...