Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKukan Da Ake Yi Kan Karin Kuɗin Wutar Lantarki Ga Masu Amfani...

Kukan Da Ake Yi Kan Karin Kuɗin Wutar Lantarki Ga Masu Amfani Da Layin Band A Ya Fito Ne Daga Wadanda Ba Sa Biyan Kudin Wutar A Baya.

Date:

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce kukan da ake yi kan karin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da layin Band A ya fito ne daga wadanda ba sa biyan kudin wutar a baya.

Adelabu, ya bayyana hakan a taron da aka yi kan Kasuwar Makamashi na Afirka karo na 8 a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce sabon tsarin farashin makamashi ya haifar da rage farashin lantarki ga masu amfani da rukunin Band A da kashi 30 zuwa 40 cikin ɗari.

Ministan ya yi zargin cewa, sabon kudin fiton ya sa aka kara kudin da ake samarwa ga masana’antun, wanda hakan ya janyo tsadar kayayyaki da ayyuka.

Ya ce karin kudin wutar lantarkin ba wai an yi niyyar ne haka kawai ga ’yan Najeriya ba, ko kuma kara tabarbarewar tattalin arzikin kasa da ya riga ya yi sanadin hauhawar farashin kayayyaki da rage darajar Naira ba

Amma anyi niyya ne don magance ko rage wahalhalun da jama’a ke ciki.

Latest stories

Related stories