Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu Ta Kori Ƙarar Bashir Ahmad.

Kotu Ta Kori Ƙarar Bashir Ahmad.

Date:

Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta yi watsi da karar da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya shigar gabanta.

 

Bashir Ahmad dai yana kalubalantar nasarar Abdullahi Mahmud Gaya a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a mazabar Gaya, Ajingi, Albasu a watan Mayun da ya gabata.

 

A hukuncin da alkalin kotun mai shari’a A.A Liman ya yanke yau Laraba, yace Bashir Ahmad ya kasa tabbatar da zargin dangwale kuri’un da wadanda basu kamata su yi zaben ba, suka yi tare da zargin hana wakilansa 85 shiga wurin zaben.

 

Don haka alkalin yace dole ne Bashir din ya bayar da gamshashiyar hujja, ba tare da kokwanto ba, tinda ya gaza yin hakan.

Latest stories

Related stories