Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu Ta Aike Da Danbilki Kwamanda Gidan Yari Kan Kalaman Tarzoma a...

Kotu Ta Aike Da Danbilki Kwamanda Gidan Yari Kan Kalaman Tarzoma a Kano

Date:

Wata kotun majistare a nan Kano ta aike da Abdulmajid Danbilki Kwamanda gidan yari bisa zarginsa da yin kalaman da ka iya tayar da tarzoma a cikin al’umma.

Tun da farko rundunar tsaron farin kaya ta DSS ce ta gayyaci Danbilki Kwamandan, kafin daga bisani ta gurfanar da shi gaban kotun da ke unguwar Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma.

Sai dai jim kadan da tura shi gidan yarin Danbilki Kwamanda ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, gwamnatin Kano ce ta gurfanar da shi ba hukumar DSS ba.

Ana tuhumarsa da batawa tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso suna, kan zargin cewa ya umarci gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi kokarin rushe masarautun da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro tare kuma da yin kalaman da ka iya tayar da tarzoma a jihar Kano.

Danbilki dai, zai gaba da zama a gidan yari har zuwa ranar Litinin din makon gobe 29 ga watan Janairu.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...