Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaKungiyar Sanatocin Arewa Ta Sha Alwashin Bibiyar Hakkokin Yankin Da Ake Kokarin...

Kungiyar Sanatocin Arewa Ta Sha Alwashin Bibiyar Hakkokin Yankin Da Ake Kokarin Karkatar Wa

Date:

Kungiyar sanatocin Arewa ta sha alwashin bibiyar hakkokin yankin na Arewa da ake kokarin karkatar wa.

Wata sanarwa da kakakin kungiyar kuma sanatan Kano ta Kudu, Sulaiman Kawu Sumaila ya fitar, ta ce kungiyar sanatocin ta bayyana haka ne lokacin da take mayar da martani kan wasu matakai da gwamnatin tarayya ta dauka na bai wa kudancin kasar nan fifiko akan wasu abubuwa, da suke hakkin kasa ne gaba daya.

Kungiyar ta ce batutuwan dai sun hada da bai wa kudancin kasar nan fifiko akan kasafin kudin shekarar bana, dauke hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa FAAN da dauke wasu manyan ofisoshin babban bankin kasa CBN daga Abuja zuwa jihar Legas.

Kungiyar tace ta karbi korafin al’ummar arewa ta fannoni da dama, saboda haka ya zama wajibi ta bibiyi lamarin domin tabbatar da cewa matakan da gwamnatin tarayya ta dauka basu cutar da Arewar ba.

Kawu Sumaila ya kara da cewa, kungiyar za ta hada hannu da dukkan bangarorin da ya kamata, domin ganin an kwato wa Arewa hakkinta, kamar yadda dokar kasa ta tsara.

Sanarwar ta bukaci al’ummar Arewa su kwantar da hankalinsu, domin abi batun ta hanyar maslaha ko kuma ta hanyar daukar mataki na shari’a.

Latest stories

Related stories