Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu a Kano ta yankewa Dan Hisbah hukuncin kisa

Kotu a Kano ta yankewa Dan Hisbah hukuncin kisa

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Babbar kotun tarayya da ke Kano ta yankewa wani Dan Hisba Dayyabu Muhammad hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kisan budurwarsa.

 

Mai shari’a Amina Adamu ce ta yanke hukuncin bayan samunsa da laifi ranar Laraba.

 

Idan za a iya tunawa tun a ranar 11 ga Janairu shekarar 2011 ne akayi zargin Dayyabu da aikata kisan kan a lokacin Yana jami’in hukumar Hisbah.

 

An dai zarge shi da yin amfani da wuka mai kaifi ya lallaba cikin dakinta tana bacci ya yayyanketa ajikinta da yarta karama.

 

Haka nan kotun ta ce bayan nazartar shari’ar, ta gano sukar da akayiwa matar da gangane kuma anyi niyyar hallakata ne.

 

Ko da dai wanda ake karar ya musanta zargin aikata kisan inda ya ce shi yana Zaria ma lokacin kisan.

 

Sai dai kotun ta ce la’akari da shaidu, ta tabbatar da cewa shi ne yayi kisan.

 

A don hakan ne ma mai shari’a Amina Adamu ta ce ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Latest stories

Related stories