Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyar bisa zargin hannu wajen lalata allunan tallace-tallace da fastocin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu ’yan siyasa a jihar.
Kwamishinan ’yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan matakan tsaro da kuma dokar da ta haramta hawan dawakai a bainar jama’a a Kano.
Bakori ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike kan lalata kadarori a lokacin da ake samun tashin hankali dangane da hawan dawakai da jerin gwanon jama’a.
Ya ƙara da cewa an kammala binciken waɗanda ake zargin tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakin doka kan duk wanda aka samu da hannu wajen aikata laifukan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.
Kamen na zuwa ne bayan wata fitowa da Sarki Aminu Ado Bayero ya gudanar a ranar Lahadi, inda rahotanni suka nuna cewa wasu daga cikin mutanen da suka raka shi sun lalata fastoci da allunan tallan Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran ’yan siyasa.
Lamarin ya ƙara tayar da hankula a jihar, yayin da rikicin masarautar Kano ke ci gaba da ɗaukar sabon salo.
