Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciKamfanin Ɗangote ya musanta raɗe-raɗin karya farashin buhun siminti

Kamfanin Ɗangote ya musanta raɗe-raɗin karya farashin buhun siminti

Date:

kamfanin Ɗangote ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya karya farashin buhun siminti da kashi 50.9% daga ranar 1 ga watan Oktoba.

A wani saƙo da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta daban-daban, wanda ya haɗa da Whatsapp, an ce wai Ɗangote na shirin rage farashin siminti a faɗin kasar nan.
Da yake jawabi ga wakilin jaridar Legit Hausa, jami’in hulɗa da jama’a na rukunin masana’antun Ɗangote, Anthony Chiejina, ya bayyana rahoton da labarin ƙanzon kurege.

Ya bayyana cewa rahoton da ake yaɗawa na karya farashin simintin Ɗangote a faɗin kasar nan ba gaskiya bane.

Jita-jitar rage farashin simintin Ɗangote na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban rukunin kamfanonin BUA , Abdul-Samad Rabiu ya fitar da sanarwar kamfaninsa ya kudiri aniyar karya farashin buhun siminti daga N5,500 da ake siyarwa a yanzu zuwa tsakanin N3,000 zuwa N3,500.

Latest stories

Related stories