Saurari premier Radio
29.1 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Najeriya ta fitar da jadawalin tsare-tsaren bukukuwan bikin cikar kasar nan...

Gwamnatin Najeriya ta fitar da jadawalin tsare-tsaren bukukuwan bikin cikar kasar nan shekaru 63

Date:

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da jadawalin tsare-tsaren bukukuwan bikin cikar kasar nan shekaru 63 da samun ’yanci wanda zai kama ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba.
Sakataren gwamnatin tarayya Mr George Akume ne ya sanar da hakan jiya Litinin yayin taron manema labarai a birnin Abuja.
Sai dai ya ce a bana za a yi bikin ne ba tare da shagulgula ba kamar yadda aka saba, sannan kuma ba za a gayyaci shugabanni daga wasu kasashe ba.
Sanata George Akume ya ce, shugaban kasa ne ya bayar da izinin gudanar da bikin ba tare da yin hidindimu ba sakamakon yanayin matsin tattalin arziki.
Yace daga cikin abubuwan da za a gudanar domin sheda wannan rana ya hada da taron manema labarai na duniya wanda shi ne aka gudanar a ranar Litinin.
Za a kuma gabatar da kasidu da muhawara kan shekaru 63 na kasancewar Najeriya kasa mai ’yanci a ranar alhamis a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa.
Sai kuma taron lacca a babban masallaci na kasa dake Abuja a ranar juma’a, sai ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba, shugaba Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasa, yayin da kuma da misalin karfe 10 na safiyar Lahadin za a gudanar da addu’o’i a cibiyar mabiya addinin Krista ta kasa dake Abuja.
A ranar Litinin 2 ga watan Oktoba, za a gudanar da fareti na musamman a fadar shugaban kasa.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...