
Aminu Abdullahi Ibrahim
Wani kwamitin zaman lafiya da Amurka ke jagoranta ya yi gargaɗin cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza na iya rushewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Kwamitin ya bayyana hakan ne a wani rahoto da ya miƙa wa kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya nuna damuwa kan ci gaba da faɗace-faɗace da kuma jinkirin aiwatar da sharuɗɗan yarjejeniyar.
Rahoton ya ce akwai babban gibi tsakanin abubuwan da aka amince da su a yarjejeniyar da kuma abin da ke faruwa a zahiri a Gaza.
Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan hare-haren Isra’ila da kuma takunkumin da ke hana shigar da kayan agaji da wasu muhimman kayayyaki zuwa yankin.
Ya ce halin da ake ciki na ƙara jefa Falasɗinawa cikin matsanancin ƙunci, musamman yayin da lokacin sanyi ke gabatowa, inda dubban mutane ke zaune a tantuna da gine-ginen da suka lalace.
Yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki ne a ranar 10 ga Oktoba, 2025, amma rahotanni sun nuna cewa hare-hare sun ci gaba duk da yarjejeniyar.
