Shugabannin kungiyoyin kwadago da na ‘yan fansho a Najeriya sun amince da marawa takarar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf baya, domin ya zarce karo na biyu a zaɓen gwamna na shekarar 2027 mai zuwa.
Sun bayyana matsayar tasu ne yayin bikin biyan tsoffin’ yan fansho haƙƙoƙinsu karo na, wanda gwamnatin ke yi, inda ƙara biyan su naira biliyan 5, wanda kawo yanzu adadin kuɗin da aka biya su ya kai biliyan 37.
Daga cikin waɗanda suka bayyana goyon bayansu ga gwamnan akwai tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Comrade Ayuba Wabba; mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comrade Kabiru Ado Minjibir; shugaban ƙungiyar ‘yan fansho ta ƙasa, Comrade Mazi Goodwin Abumisi; da shugaban NLC na Kano, Comrade Kabiru Inuwa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na jaddada cewa gwamnatin Kano tana ƙoƙarin kammala biyan dukkan basussukan haƙƙoƙin ‘yan fansho da suka yi ritaya kafin watan Afrilun 2027.
