Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya zargi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da guje wa zuwa Amurka saboda fargabar yiwuwar kama shi.
Okonkwo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Prime Time na Arise News, inda yake magana kan rashin halartar Tinubu taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81, UNGA, da ake gudanarwa a birnin New York.
A cewarsa, Tinubu bai halarci taron UNGA da kansa ba tsawon shekaru uku a jere, inda a wannan karon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Najeriya.
Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin, tana mai cewa rashin Tinubu a taron ba shi da wata alaƙa da fargabar kama shi a Amurka.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu na ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati daga wajen kasar, yana mai cewa batun bayanan da hukumomin Amurka ke riƙe da su game da Shugaban Ƙasar, wanda ya shafi wani al’amari na kwace kuɗi a shekarar 1993, ba shari’ar laifi ba ce.
Onanuga ya bayyana cewa batun neman waɗannan bayanai ne ƙarƙashin dokar Freedom of Information Act (FOIA).
Haka kuma, Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce babu wata sanarwa daga gwamnatin Amurka da ta nuna cewa an hana Tinubu shiga ƙasar ko kuma yana fuskantar barazanar kama shi.
Fadar Shugaban Ƙasar ta ce Tinubu ya bar Najeriya tun ranar 30 ga Agusta, inda ya ziyarci Faransa tare da halartar wasu taruka, kafin daga bisani ya wakilta Shettima a taron UNGA.
