
Daga Khalil Ibrahim Yaro
‘Yan Majalisun sune Ali Madakin Gini da Sani Rogo da kuma Alhassan Rurum a matsayin ladabtarwa
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar Sanatan ne da kuma ‘Yan Majalisar Wakilan 3 ne a wani na dauki matakin ladabtarwa.
Shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin.
Jam’iyyar ta dauki matakin dakatarwar ne a bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa manufofin jam’iyyar.
“Duk da cewa jam’iyyar ta ba su tikitin takara kyauta a lokacin zabe, wasu daga cikinsu sun aikata abubuwan da su ka saba da manufofi, ka’idoji da kuma tsarin jam’iyyar” in ji shi
Shugaban jam’iyyar a kano ya bayyana cewa, jam’iyyar ta nuna rashin jin dadinta kan halayen wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar.
Sanata Kawu Sumaila shi ne mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattijai, Alhaji Abdullahi Sani Rogo kuma dan Majalisar Wakilai ne mai wakiltar mazabar Rogo.
Alhassan Rurum na wakiltar Rano da Kibiya ne haka shi ma Ali Madakin Gini yana wakiltar mazabar Dala duk a Majalisar Wakilai.