Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJagoran ƙungiyar Ecowas kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shawarci sojojin da...

Jagoran ƙungiyar Ecowas kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shawarci sojojin da ke mulki a Nijar, su mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya a cikin wata tara, kamar yadda Najeriya ta yi a shekarun 1990

Date:

Jagoran ƙungiyar Ecowas kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shawarci sojojin da ke mulki a Nijar, su mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya a cikin wata tara, kamar yadda Najeriya ta yi a shekarun 1990.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar na cewa a zamanin Janar Abdulsalami Abubakar cikin 1998, an kafa kwamitin miƙa mulki cikin wata tara, kuma kwamitin ya yi nasarar mayar da ƙasar kan tafarkin dimokradiyya.

Don haka, Shugaba Tinubu ya ce bai ga dalilin da zai sa a kasa yin haka a Nijar ba, matuƙar sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar, da gaske suke yi.

Tinubu na wannan jawabi ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasar a ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji sa’ad Abubakar lll.

”Mai Alfarma, kada ka gaji don Allah, za ka sake koma wa Nijar. Ba za a amince da halayyar sojojin ba.

Idan suka yi sauye-sauye cikin gaggawa, to mu ma cikin hanzari za mu sassauta takunkuman da muka ƙaƙaba musu, domin rage wahalhalun da muke gani a ƙasar”, in ji shugaban na Ecowas.

Ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumai, tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi ranar 26 ga watan Yuli.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...