Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano Ta Musanta Cewa Ta Kwace Tashar Mota Ta Rijiyar Zaki

Gwamnatin Kano Ta Musanta Cewa Ta Kwace Tashar Mota Ta Rijiyar Zaki

Date:

Gwamnatin Kano Ta Musanta Cewa Ta Kwace Tashar Mota Ta Rijiyar Zaki
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnan jihar Kano ya fitar.

Yace labarin bashi da tushe balle makama, kuma masu yada jita-jitar suna kokarin kawar kawo rudani ne a alamuran gwamnatin.

Wannan jawabin ya biyo bayan yaduwar jita-jitar dake cewa gwamnatin jihar Kano ta yanka tashar mota ta Rijiyar Zaki.

Sanusi Bature yace mazauna yankin ne suka bukaci a chanja amfanin filin daga filin kasuwanci zuwa filayen zaman alumma sandiyar karuwar aikata laifuka da tashe-tashen hankulan da suke fuskanta.

Yace gwamnatin bata yanke hukunci game da tashar Rijiyar zakin ba kuma zata sanarwa alumma matakin data dauka da zarara ta yanke hukunci.

A halin yanzu kudurin chanja amfanin filin yana gaban hukumar tsara birane KANUPDA domin tantance yiwuwar maida filin tashar daga filin kasuwanci zuwa filayen zaman alumma

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...