Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiIvory Coast ta karbi sabuwar allurar rigakafin zazzabin maleriya.

Ivory Coast ta karbi sabuwar allurar rigakafin zazzabin maleriya.

Date:

An kai kashin farko na allurar rigakafin cutar maleriya da Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da ita zuwa Ivory Coast.

Allurar rigakafin wadda wata tawaga a jami’ar Oxford ta samar da ita, ta zamo ta farko da ta samu karbuwa da kashi 75 cikin 100.

Masana kimiyyar da suka samar da rigakafin sun ce allurar za ta iya ceton rayukan mutane dubu 300 a shekara.

Wannan sabuwar allurar rigakafin ita ce ta biyu da aka samar domin magance cutar maleriya wadda ke janyo mutuwar mutane kusan dubu dari biyar a shekara yawancinsu kananan yara.

A wani labarin Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya wasu sabbin takunkumai a kan Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi ‘yan kama wuri zauna da ke zaune a GaÉ“ar Yamma da Kogin Jordan.

Takunkuman za su shafi wasu Isra’ilawa biyar ne da kuma wasu kungiyoyi uku, waÉ—andaa Tarayyar Turai ta ce sun Æ™untata wa FalasÉ—inawa ta hanyar take haƙƙinsu.

Ƙungiyoyin da abin ya shafa sun hada da wata ƙungiya da ake kira Tzav-9, da ake zargi da hana manyan motocin agaji shigar da kaya zuwa Gaza.

ÆŠaya daga cikin mutanen da takunkumin ya shafa kuma shi ne Ben-Zion Gopstein, wanda ya samar da kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta Lehava.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...