Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, ta cire bayanan masu zaɓe miliyan ɗaya da dubu ɗari shida da tara da ɗari biyar da talatin da uku daga rajistar masu zaɓe.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, da yake bayyana hakan ya ce an cire rajista miliyan ɗaya da dubu ɗari shida da takwas da ɗari shida da sittin saboda rashin inganci, yayin da sauran mutum 873 suka rasu.
Ya ce binciken ya gano rajista fiye da ɗaya, amfani da hotunan bogi da aka sarrafa ta fasahar AI, da kuma wasu kura-kurai a tsarin rajistar.
Hukumar ta kuma gano mutane 54 daga jihohi goma da ake zargi da hannu wajen aikata ba daidai ba a lokacin rajistar, inda ta ce za ta ɗauki matakan ladabtarwa a kansu, ciki har da gurfanar da waɗanda abin ya shafa a gaban kotu.
INEC ta kuma haramta amfani da kyamarorin yanar gizo na waje wajen ɗora hotunan masu rajista, tare da umartar cewa dole ne a ɗauki hotuna ta hanyar manhajar da hukumar ta amince da ita.
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da tantance tsoffin bayanan rajista domin gano da kuma cire waɗanda ba su inganta ba gabanin zaɓen shekarar 2027.
