Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Ƙasa da Ƙasa (International Human Rights Commission — IHRC) ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatocin wasu jihohin Najeriya da suka ƙi amincewa da biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane.
Hukumar ta ce ci gaba da biyan kuɗin fansa na ƙarfafa gwiwar ’yan bindiga wajen ci gaba da satar mutane domin samun kuɗi, lamarin da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a ƙasar.
Haka kuma, hukumar ta buƙaci gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da su inganta hanyoyin tattara bayanan sirri da dabarun tsaro domin dakile ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
Shugaban hukumar na ƙasa, Ambasada Abdullahi Adamu Bakoji mai ritaya, ya yi ikirarin cewa kashi 95 cikin 100 na ayyukan ta’addanci ana aikata su ne domin neman kuɗin fansa, yana mai cewa dakile biyan kuɗin fansa na iya taimakawa wajen rage matsalar.
Ambasada Bakoji ya ƙara da cewa kawo ƙarshen tashe-tashen hankula a Najeriya na buƙatar gwamnati da hukumomin tsaro su samar wa jami’an tsaro ingantattun kayan aiki da bayanan sirri domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
