Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi alkawarin cewa gwamnatin jam’iyyar za ta dawo da tallafin man fetur tare da rage tsadar rayuwa idan ta samu nasara a zaɓen 2027.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Amaechi, tsohon gwamnan Jihar Rivers, ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da jama’a na jam’iyyar ADC da aka gudanar a birnin Benin a ƙarshen makon nan.
Amaechi ya ce tsarin tattalin arziƙin da jam’iyyarsa ke shirin aiwatarwa zai mayar da hankali kan ƙarfafa tace man fetur a cikin gida da kuma rage farashin man fetur.
A cewarsa, rage farashin man fetur zai taimaka wajen saukar da kuɗin sufuri, wanda hakan zai rage nauyin tsadar rayuwa da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Ya ƙara da cewa rage kuɗin sufuri zai taimaka wajen saukar da farashin kayayyaki tare da sauƙaƙa wa iyalai biyan buƙatunsu na yau da kullum.
Tsohon gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin ADC za ta faɗaɗa damar samun ilimi ta hanyar gina ƙarin makarantu.
Dangane da zaɓen gwamnan Jihar Edo, Amaechi ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin ADC za ta ba su damar zaɓar wanda suke so cikin ’yanci, ba tare da an ɗora musu wanda ba su zaɓa ba.
Ya kuma gargaɗi masu zaɓe da kada su ƙaurace wa rumfunan zaɓe, yana mai cewa alhakin samar da sauyin da suke buƙata yana hannunsu.
