Hukumar Shari’a ta Kano ta bayyana cewa ba za ta lamunci ganin yadda ake ci gaba da buɗe masallatan Juma’a a lunguna da sakunan jihar ba tare da samun amincewarta ba.
Kwamishina na biyu a Hukumar, Sheikh Ali Danabba, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai.
Sheikh Ali Danabba ya ce doka ta tanadi cewa duk wanda ke son buɗe masallacin Juma’a dole ne ya fara neman izini daga Hukumar Shari’a tare da cika sharuddan da aka gindaya.
Dan Abba ya jaddada cewa Hukumar ba za ta amince da duk wani yunƙuri na buɗe masallatan Juma’a ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba, yana mai kira ga al’umma da su mutunta dokoki da tsare-tsaren da aka kafa domin tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da harkokin ibada a jihar.
Sheikh Ali Danabba ya ce Hukumar su zata ci gaba da sanya ido a al’amuran da suka shafi addini domin tabbatar da komai yana tafiya yadda ya kamata.
