Hukumar Shari’a ta Kano ta nemi haɗin kan malaman addinin Musulunci na jihar domin lalubo hanyoyin gyaran tarbiyyar matasa, da dakile munanan kalamai da cin mutuncin da wasu ‘yan siyasa ke yiwa junansu a shafukan sada zumunta.
Shugaban hukumar, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci tawagar hukumar ziyarar yin rangadi ga wasu fitattun malaman addinin Musulunci a kano.
Ziyarar hukumar ta fara ne a gidan Sheikh Abdulwahab Abdullah, kafin ta wuce ofishin shugaban Majalisar Malamai Sheikh Ibrahim Khalil, da kuma shugaban Ƙadiriyya na Afirka, Sheikh Ƙariballah Sheikh Nasiru Kabara.
A yayin ziyarar, Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali Ɗanabba, ya buƙaci malamai da limamai, da su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma kan matsalolin da ke addabar kano, musamman illar bidiyon Raƙumin AI da ke ɗauke da kalaman batsa wanda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.
A nasa jawabin, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce Majalisar Malaman za ta yi ƙoƙarin haɗa kan limamai da malamai domin ba da gudummawa wajen gyaran tarbiyyar al’umma, yayin da Sheikh Ƙariballah Sheikh Nasiru Kabara ya buƙaci hukumomin Hisbah, Shari’a, Zakka, Majalisar Shura da Majalisar Malamai su haɗa kai wajen gudanar da zama na musamman domin lalubo hanyoyin magance matsalolin tarbiyya.
Shi ma Sheikh Abdulwahab Abdullah ya bayyana wasu hanyoyin da za’a bi wajen magance matsalolin da ake fuskanta a, yayin da hukumar Shari’ar ta sha alwashin ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin inganta tarbiyya da samar da ci gaba a Kano.
