
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman kansu ta Jihar Kano ta sake buɗe makarantar Prime College daga ranar Litinin 23 ga watan Nuwambar da muke ciki bayan rufe ta na tsawon kwanaki biyar.
Sakataren zartarwa na hukumar, Comrade Baba Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano.
Ya ce hukumar ta rufe makarantar ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, saboda rashin bin ƙa’idojin sabunta takardun rajista da kuma sake tabbatar da takardar shaidar izinin gudanar da aiki, wato Certificate of Operation.
Sai dai ya ce hukumar ta sake duba matakin bayan wasu manyan mutane sun shiga tsakani, tare da neman afuwa daga mahukuntan makarantar da kuma amincewarsu da ɗaukar alhakin wasu kura-kuran gudanarwa da aka samu.
Baba Abubakar Umar ya bayyana cewa sake buɗe makarantar na da sharadin kammala sauran buƙatun sake tabbatar da takardun izinin aiki, gabatar da takardar alƙawarin bin ƙa’ida, inganta tsarin gudanarwa da kuma biyan harajin da doka ta tanada na shekarar karatu ta 2026/2027.
Ya jaddada cewa matakin sake buɗe makarantar ba yana nufin hukumar ta sassauta ƙa’idojinta ba ne, sai dai ta yi la’akari da adalci da kuma makomar ɗalibai.
Sakataren ya kuma yi kira ga masu makarantun zaman kansu a jihar Kano da su ba da cikakken haɗin kai wajen gudanar da aikin sake tantance takardun izinin aiki, yana mai cewa bin ƙa’idojin hukumar wajibi ne ga dukkan makarantu ba tare da la’akari da girmansu ko matsayinsu ba.
Ya ce manufar hukumar ba ita ce rufe makarantu ba, sai dai tabbatar da cewa dukkan makarantu suna gudanar da ayyukansu bisa doka tare da cika ƙa’idojin da aka gindaya.
