Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar Hisba Ta Fara Kamen Yan Mata Masu Tallan Dare A Jihar...

Hukumar Hisba Ta Fara Kamen Yan Mata Masu Tallan Dare A Jihar Kano.

Date:

Hukumar Hisbah ta samu nasarar kama wasu ’yan mata masu karancin shekaru a tashar motar Sabontiti da ke yankin karamar hukumar Kumbotso.

 

Babbar jami’ar da ta jagoranci aikin kamen, Malama Rabi Bello, ta ce dimbin ‘yanmatan da ke yawo a gefen titina abun tsoro ne.

 

Idan za a iya tunawa, a watan Disambar bara, mataimakiyar kwamandar Hisbah bangaren mata, Malama Kulsum Kasim, ta jagoranci wata tawaga, inda aka kwashe mata masu sana’ar tallar dare a wasu titunan kananan hukumomin jihar Kano.

 

A wancan lokaci an ga yan mata masu talla a kasuwanni, da wuraren shakatawa, da tashar motoci, da garejin kanikanci, da sauran wurare da daddare.

 

Yayin da suke yaba kokarin da hukumar Hisbah ke yi, ‘yan kasuwa a tashar mota sun yi kira ga iyaye su daina tura yayansu, musamman yan mata zuwa kasuwanni da wuraren ajiye motoci domin saye da sayarwa da dare.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...