Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaHarin Kaduna: Asibitin kashi na Dala zai yiwa marasa lafiya aiki kyauta

Harin Kaduna: Asibitin kashi na Dala zai yiwa marasa lafiya aiki kyauta

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Asibitin Kashi na Dala ya bayyana aniyarsa na yiwa wadanda harin jirgin kasan Kaduna-Abuja ya rutsa da su magani kyauta.

Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan gudanarwa na asibitin. Mal. N Harazumi ya sawa hannu.

Harazumi yace aikin zai kasance ne karkashin umarnin ma’aikatar lafiya ta kasa.

Sanarwar da aka aikewa dukkanin shugabannin bangarorin asibitin ta bukaci su yiwa duk wanda aka kawo bangarensu aiki kyauta.

Idan za a iya tunawa a ranar 28 ga Maris me yan ta’adda suka sanya bom akan hayar titin Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da yayi sanadiyyar hallaka da jikkata mutane da dama.

Latest stories

Related stories