Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta kama mutum 12 da ake zargi da hannu a ayyukan garkuwa da mutane da taimaka wa masu aikata laifuka, yayin wani samame da jami’an tsaro suka gudanar a yankunan Millennium City da Maraban Rido.
Rundunar ta ce cikin waɗanda aka kama akwai mutum takwas da ake zargi da garkuwa da mutane, da wasu huɗu da ake zargin masu kai wa ’yan bindiga bayanan sirri ne, ta kuma ce an ƙwato bindigogin ƙirar AK-47 yayin samamen.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansur Hassan, ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin garkuwa da mutane da suka haɗa da Dauda Murna, Usman Abdullahi, Abubakar Sulaiman, Saleh Abdullahi, Usman Muhammed, Mathias Moses, Makama John da Tafarki Audu.
Sauran huɗun da ake zargin masu kai bayanan sirri ne sun haɗa da Shu’aibu Sabiu, Audu Makama, Simon Moses da Amadu Mathew, rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa biyu daga cikin waɗanda ake zargin sun amsa zargin fallasa bayanan sirrin ayyukan jami’an tsaro ga masu aikata laifuka, sai dai ba ta bayyana sunayensu ba.
A wani mataki na ƙarfafa tsaro, rundunar ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta ƙara mata motocin yaƙi masu sulke guda uku domin taimaka wa jami’an wajen gudanar da ayyukansu a Millennium City da sauran yankunan da ke kusa.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Muhammad Rabiu, ya kuma bayar da umarnin tura ƙarin jami’ai na musamman da motocin aiki zuwa yankunan domin ƙarfafa sintiri da sa ido, tare da inganta saurin kai ɗauki, rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a laifukan, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.
Rundunar ta buƙaci mazauna yankunan da su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani motsi da suke zargi ga jami’an tsaro, ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da kai samame domin dakile garkuwa da mutane da sauran laifuka a jihar.
