Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhume-tuhume takwas da gwamnatin Tarayya ta shigar kan Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da kikrkirar sabuwar hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council PFIPC tare da zama matsayin babban daraktan ta.
Mai shari’a Mohammed Garba Umar ne ya yi watsi da tuhume-tuhumen, bayan Gwamnatin Tarayya ta shigar da buƙatar cewa za a mayar da Adeyemi zuwa Babbar Kotun Abuja domin sake gurfanar da shi.
A zaman kotun na jiya Litinin, jagoran Masu Gabatar da Ƙara na Tarayya Rotimi Oyedepo, SAN, ya bukaci a kawo ƙarshen shari’ar.
Oyedepo ya shaida wa kotun cewa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a ya sake nazarin fayil ɗin shari’ar Adeyemi da kuma tuhume-tuhumen da babban sufetan ’Yan Sanda ya fara shigarwa, inda aka gano wasu kurakurai a cikinsu.
Ya ce takardun da ake zargin Adeyemi ya yi wa jabun hannu ko ya ƙirƙira na bogi a lokacin da yake gudanar da ayyukan wannan hukuma da ake zargin ta bogi ne, sun ƙunshi laifuffukan da Babbar Kotun Abuja ce ke da ikon sauraro da hukunta su.
Lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu, SAN, bai yi adawa da buƙatar ba, wanda hakan ya sa Mai shari’a Umar ya yi watsi da tuhume-tuhumen da aka shigar a kotun.
Adeyemi, mai shekaru 38, yana fuskantar shari’a tare da wasu mutane biyu da ake zargin ba a san inda suke ba, wadanda ake tuhuma da laifukan haɗa baki wajen aikata laifi da kuma yin jabun takardu.
