Gwamnatin Kano ta ce za ta fara aikin gina gidaje 50 a gefen titunan kilomita 5 da ake ginawa a dukkan ƙananan hukumomi 36 na jihar, domin rage gibin gidaje da bunkasa yankunan karkara.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki na yini guda, wanda aka shirya domin tattauna hanyoyin tabbatar da gudanar da aikin cikin sauki, musamman kan batun biyan diyya ga masu filaye da warware korafe-korafe.
Gwamnan wanda Kwamishinan raya karkara da Dr Abdulkadir Abdussalam, ya wakilta ya ce kowane aikin zai kasance tare da muhimman abubuwan more rayuwa, ciki har da asibiti, kasuwa da ofishin ‘yan sanda.
Kwamshinan ya ce shirin mai taken 5km Abba Gida Gida Rural Model Cities, zai taimaka wajen samar da ingantattun matsugunai tare da bunkasa ababen more rayuwa da tattalin arzikin al’ummomin karkara a kananan hukumomin jihar 36.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, a nasu bangaren, Kwamishinan Gidaje, Arch. Ibrahim Yakubu, da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Alhaji Muhammad Tajuddeen Othman, sun yabawa shirin, yayin da shugabannin kananan hukumomi 36 suka bayyana goyon bayansu domin ganin an fara aikin tare da kammala shi cikin lokaci.
