Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin Kano ta sake gabatar da sabbin zarge-zarge kan tsohon gwamna Abdullahi...

Gwamnatin Kano ta sake gabatar da sabbin zarge-zarge kan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Date:

Sati daya bayan babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta fara sauraron tuhumar da ake yiwa tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.

Gwamnatin Kano ta sake gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan a gaban wata babbar kotun jiha.

A sabbin zarge zargen dai ana tuhumar Ganduje da tsohon kwamishinan shari’a Barista Musa Abdullahi Lawan da karkatar da kudi kimanin naira miliyan 240.

Sai dai kotun bata sanya ranar fara sauraron sabbin tuhume-tuhumen da ake yiwa Abdullahi Umar Gandujen ba.

Idan za a iya tunawa Abdullahi Umar Ganduje da maidakin Farfesa Hafsat Ganje sun kauracewa zaman kotun da akyi kan zarge zargen da ake yi musu.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...