Gwamnatin Kano ta ce ayyuka 80 cikin 106 da ta duba a kananan hukumomi shida na jihar sun kai matakin kammalawa dari bisa dari, yayin da wasu 20 ke ci gaba da gudana, sannan aka bayar da kwangilar wasu guda shida, wanda jimillar kuɗin ayyukan ya zarce biliyan 48.
Kwamishinan ma’aikatar bibiyar ayyukan gwamnatin Kano Kwamared Nura Iro Maaji, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira.
Ma’aji ya ce ƙananan hukumomin da aka kammala ayyukan sun haɗar da Kabo, Tofa, Dawakin Tofa, Bagwai Shanono da Gwarzo.
Kwamishinan ya ce ayyukan da aka duba a watan Satumba sun hada da tituna, makarantu, asibitoci, ofisoshin tsaro, fitilun kan titi da samar da ruwan famfo a kananan hukumomin Kabo, Dawakin Tofa, Tofa, Shanono, Gwarzo da Bagwai.
Ma’aji ya ce ma’aikatar ta kuma samar da wani tsari na yanar Gizo wanda zai baiwa al’ummar Kano damar bibiyar ayyukan da gwamnati ke gudanarwa da kan su, da kuma tsarin bin diddigin dukkan ayyukan da sauran ma’aikatun gwamnatin Kano suke gudanarwa musamman a bangaren bayar da kwangila.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Maaji na cewa ma’aikatar ta sa za ta ci gaba da sanya ido kan ayyukan gwamnati a kananan hukumomi 44 na jihar, tare da bibiyar wadanda suka samu tsaiko ko matsalolin inganci, tare da karfafa amfani da tsarin fasahar zamani wajen sa ido kan ayyuka.
