Hukumar Shari’ar Addinin Musulunci ta Jihar Kano ta umarci direbobin baburan adaidaita sahu da su daina ɗaukar mata a gefen hagu ko dama na babur, abin da aka fi sani da “Attachment”, tana mai cewa wannan ɗabi’a ta saɓa wa koyarwar addinin Musulunci saboda cuɗanya tsakanin namiji da macen da ba muharramarsa ba.
Kwamishinan na biyu na hukumar, Sheikh Ali Ɗanabba, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin Ƙungiyar Direbobin Baburan Adaidaita Sahu ta VOTORA a ranar Alhamis, 30 ga Yuli, 2026.
A yayin taron, bangororin biyu sun tattauna hanyoyin inganta tsari da tsafta a harkar sufurin baburan adaidaita sahu, tare da rawar da direbobi za su taka wajen tallafa wa hukumomi wajen yaƙi da sha da dillancin miyagun ƙwayoyi, sace-sacen yara, da kuma ƙarfafa tsaro a faɗin Jihar Kano.
Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma sanar da cewa Hukumar Shari’ar Addinin Musulunci za ta shirya zama na musamman da ƙungiyoyin direbobin baburan adaidaita sahu domin gudanar da wa’azi da wayar da kai kan muhimmancin bin ƙa’idodin addinin Musulunci da kuma kiyaye ɗabi’u masu nagarta.
