Gwamnatin Kano ta fara rangadin duba halin da ƙananun matatun ruwa ke ciki a wasu ƙananan hukumomin jihar, domin tabbatar da ƙudirin ta na inganta samar da ruwan sha a sassan karkara.
Yayin ziyarar wadda ta kunshi manyan jami’an gwamnati, Kwamishinan Ma’aikatar ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Dahir Muhammad Hashim,
ya ce rangadin ya biyo bayan ƙaddamar da shirin farfaɗo da manyan matatun ruwa masu samar da ruwa a cikin birnin Kano da Gwamna Abba Kabi Yusuf ya yi.
Tawagar ta ziyarci matatar ruwa ta Kusalla wadda ke samar da ruwa ga ƙananan hukumomin Karaye, Kiru da Gwarzo, da matatar ruwan Pada mai samar da ruwa ga al’ummar Gwarzo.
Sai kuma, matatar ruwan Magaga wadda ke samar da ruwa ga Gwarzo da Kabo, da kuma matatar ruwan Guzuguzu mai samar da ruwa ga Kabo da Rimin Gado.
Dr Hashim ya bayyana cewa an tantance matsalolin da ke addabar matatun ruwan da aka ziyarta tare da tsara hanyoyin gyara da sabunta su domin inganta ayyukansu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na tabbatarwa da al’ummar ƙananan hukumomin Karaye, Kiru, Gwarzo, Kabo da Rimin Gado cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta yi duk mai yiwuwa wajen dawo da cikakken aikin matatun domin samar da wadataccen ruwan sha ga al’umma.
