Gwamnatin Kano ta sake jaddada cewa ƙofarta a buɗe take a kowane lokaci domin sauraron shawarwari, buƙatu da damuwar al’ummar jihar, da nufin ƙara inganta gudanar da mulki da ayyukan raya ƙasa.
Mataimakin Gwamnan Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi tawagar ƙungiyar Muryar Kano ta Kudu a ofishinsa.
Garo ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummar Kano, yana mai cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da tattaunawa da tuntuɓar jama’a domin ciyar da jihar da yankin Kano ta Kudu gaba.
Tun da farko, jagoran tawagar, Barrista Sabi’u Abdullahi Usman, ya ce ƙungiyar tasu mai wakiltar ƙananan hukumomi 16 na Kano ta Kudu ta kai ziyarar ne domin yabawa gwamnatin jihar kan ayyukan raya ƙasa da ta aiwatar a yankin.
Ya ce daga cikin ayyukan akwai gina madatsar ruwa ta Dan-Soshiya a ƙaramar hukumar Kiru, kafa Kwalejin Fasaha ta Gaya, da sauran ayyukan da suka shafi inganta ilimi da harkokin kiwon lafiya a yankin.
Wakilinmu, Kamal Umar Kurna, ya rawaito cewa ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin Kano da ta yi la’akari da gyaran wata babbar hanya da ke haɗa ƙananan hukumomi da dama a yankin Kano ta Kudu.
