Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi kira da a ƙara haɗa gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi domin yaƙi da ’yan bindiga da sauran laifukan da ke barazana ga tsaron al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Najeriya ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya jaddada cewa haɗin gwiwar hukumomin tsaro da gwamnatoci na da muhimmiyar rawa wajen magance matsalar rashin tsaro.
Ahmed Aliyu ya ce ya zama wajibi a ƙarfafa musayar bayanan sirri, daidaita ayyukan hukumomin tsaro da kuma samar da kayan aiki da ake buƙata domin dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su ba hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar bayar da sahihan bayanai kan mutanen da ake zargi da aikata laifuka, tare da kauce wa ɗaukar doka a hannu.
Gwamnan ya taya ’yan Najeriya murnar zagayowar ranar ’yancin kai, yana mai jaddada cewa samun zaman lafiya da tsaro na daga cikin muhimman ginshiƙan ci gaban ƙasa.
