Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan koyarwa da waɗanda ba na koyarwa ba na Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil da Jami’ar Northwest Kano.
Sabon tsarin albashin ya samo asali ne daga tsarin da gwamnatin Najeriya ta fara aiwatarwa a jami’o’inta, wanda zai fara aiki daga watan Janairun 2026, yayin da za’a fara biyan sabon albashin daga watan Satumbar 2026.
Gwamnan ya ce kuɗin da ake buƙata wajen biyan ƙarin albashin jami’o’in biyu, ya kai sama da naira miliyan 391 a duk wata, wanda adadin ya zarce naira biliyan 4 a duk shekara.
Haka kuma, gwamnatin ta kano ta ware sama da naira biliyan 1 a kasafin kuɗin ƙari na shekarar 2026 domin biyan kuɗin daga watan Satumba zuwa Disamba, yayin da za’a tanadi sama da Naira 3.13 a kasafin 2027 domin biyan bashin ƙarin albashin daga Janairu zuwa Agusta 2026.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Gwamna Yusuf ya kuma amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin ziyara ga jami’o’in biyu, da sauran manyan makarantun jihar, domin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da inganta tafiyar da harkokin makarantun.
