Dakarun sojin kasar Chadi sun halaka mayaƙan Boko Haram da dama tare da kama wasu bayan harin da ƙungiyar ta kai fadar shugaban ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ruwaito cewa mayaƙan sun kai hari a cikin harabar fadar shugaban ƙasar da yammacin jiya Laraba.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna sojojin suna yiwa yan Boko Haram ruwan wuta, a yayin da rahotanni ke nuni da cewa an kama wasu daga cikin mayakan suna amsa tambayoyi.
A yammacin jiya Laraba ne mazauna birnin N’Djamena suka shiga zaman ɗar-ɗar bayan sunfara jin ƙarar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasar.
Sai dai daga bisani, ministan ababen more rayuwa na ƙasar, Aziz Mahamat Saleh, ya sanar da cewa an shawo kan lamarin.
Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, ba wani abin damuwa ba ne saboda an riga an magance matsalar. Shi ma wani jami’in gwmanatin ƙasar, Abderaman Koulamallah, ya ce wata yar matsala ce kuma komai ya daidaita.