Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin ci gaba da haɗa hannu da Gwamnatin Kano, da sauran masana da masu ruwa da tsaki, wajen bunƙasa fannin ilimi a ƙasar, domin tabbatar da ganin kowane yaro a ya amfani damar samun ingantaccen ilimi.
Ministan Ilimi na ƙasar Dr Ma’aruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan, lokacin da yake ƙaddamar da sabuwar makarantar sakandaren ‘yan Mata mai suna Abba Kabir Yusuf da aka gina a ƙauyen Dangwauro a Kano.
Dr Alausa ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Kano ke aiwatarwa a fannin ilimi, wanda suka hadar da ginawa da gyaran makarantu, ɗaukar ƙwararrun malamai da faɗaɗa damar yin karatu ga yara, sune suka sanya Kano ta zama abin koyi wajen inganta ilimi a faɗin Najeriya.
Ministan ya ce aikin samar da Makarantar wani babban mataki ne wanda zai faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi ga yara mata, kuma matakin na daga cikin manufofin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na bunƙasa ilimi da ƙarawa yara mata damar zuwa makaranta domin gina al’umma mai ilimi da ci gaba.
Da yake jawabi a wajen buɗe makarantar. Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya buƙaci al’ummar Dangwauro da maƙwabtansu da su kula da makarantar yadda ya dace, yana mai jaddada cewa ilimantar da yara mata na daga cikin manyan ginshiƙan ci gaban al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, Ministan ya ƙaddamar da makarantar ne yayin ziyararsa a Kano domin halartar bikin rabon takardun ɗaukar aikin gwamnati ga sabbin malamai 4,900, da na BESDA 3,688 ƙarƙashin shirin bunƙasa ilimin yara.
