A yau Talata Shugaba Tinubu zai je jihar Jigawa, domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓensa na 2027.
Yayin ziyarar, ana sa ran shugaban ƙasar zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta gudanar a birnin Dutse, babban birnin jihar.
Ayyukan da za a ƙaddamar sun haɗa da cibiyar koyar da sana’o’i ta Bola Ahmed Tinubu Multipurpose Skills Acquisition Centre, cibiyar Renewed Hope Technical Services da kuma hanyar Garu da aka faɗaɗa zuwa tagwayen titi.
Haka kuma, ana sa ran Tinubu zai ƙaddamar da rabon taraktoci 400 da kayayyakinsu, injinan girbin amfanin gona 60 da sauran kayan aikin noma ga manoma domin bunƙasa harkar noma.
Gwamna Umar Namadi ya ce an kammala shirye-shiryen tsaro da sauran abubuwan da suka dace domin tarbar shugaban ƙasar, bayan ya zagaya wuraren da za a gudanar da ayyukan.
Sai ku ci gaba da bibiyar Premier Radio domin jin abubuwan da za su wakana yayin ziyarar shugaba Tinubu a Jigawa.
