- By Kabeer Bello Tukur
Iran ta tabbatar da rasuwar Jagoran Juyin Juya Halin kasar Ayatollah Ali Khamenei a harin Amurka da Isra’ila
Kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun tabbatar da cewa Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei, ya rasu sakamakon hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai kan ƙasar.
Kamfanonin labarai na gwamnati, ciki har da Tasnim, Mehr da Press TV, sun sanar da a daren jiya cewa Jagoran mai shekaru 85 ya “yi shahada” a yayin harin.
Ofishin Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya fitar da sanarwa yana bayyana lamarin a matsayin “babban zunubi” da ba zai wuce ba tare da daukar fansa ba.
Sanarwar ta kuma bayyana kwanaki 40 na zaman makoki a ƙasar, tana mai cewa za a ɗauki matakai masu tsauri domin tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan lifi sun dandana kudarsu
Tuni kasar ta shiga makokin kwana 40 daga yau Lahadi, sannan an bayar da hutun kwana 7.
Tun da farko Shugaban Amurka Donald Trump ya rubuta a shafinsa na Truth Social cewa Khamenei “ya mutu,” bayan Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce akwai “alamu masu karfi da ke nuna Jagoran “ba ya raye.”
