Al’ummar garin Mokwa na jihar Neja na ci gaba da alhinin rashin ƴan uwa da abokan arziƙi sakamakon ambaliyar da ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 200 sannan fiye da 500 suka ɓace.
Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta sanar da cewa kawo yanzu ambaliyar ta raba mutum fiye da 3,000 da gidajensu sannan ta lalata ɗaruruwan gidaje.
Wasu da abun ya shafa sun shaida wa BBC cewa ambaliyar ta fara da daddare ne a lokacin da jama’a ke barci wani abu da ya sa ruwan ya tafi da mutane da dama.
Tuni dai shugaba Tinubu ya umarci hukumar NEMA da ta kafa sansani domin tsugunar da waɗanda ambaliyar ta ɗiɗaita.
Gidaje fiye da 3,000 ne suka lalace sakamakon ambaliyar.
A ranar Laraba da daddare ne wata ambaliya ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja, inda ta yi sanadiyar rayuka da dama tare kuma da lalata gidaje.
Mataimakin gwamnan na jihar Neja ya ce mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar sun kai sama da 151.
Ya ce sun samu nasarar gano gawawwaki 151 zuwa yanzu.
“Na ga wasu gawawwaki 31 a garin Raba, ruwa ya kwace gadar da ta haɗa garin da Mokwa. Gidaje masu ɗimbin yawa sun rushe a wannan garin,” a cewar kwamred Yakubu.
Sai dai BBC ta gano cewa mutum sama da 200 ne suka mutu zuwa yanzu.
Rahoton da hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Nsema ta fitar, ta ce ambaliyar ta shafi magidanta sama da 500, waɗanda al’ummominsu suka kai mutum 3,000.
An ruwaito cewa wasu iyalai sun rasa ƴan uwa biyu zuwa biyar ciki har da yara ƙanana.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa alkaluman waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa bayan da ruwa ya tafi da wasu zuwa cikin kogin Neja
