Saurari premier Radio
25.1 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiFiraministan Nijar yayi Allah wadai da matakin da ƙasar Benin ta ɗauka...

Firaministan Nijar yayi Allah wadai da matakin da ƙasar Benin ta ɗauka na hana ƙasar fitar da manta.

Date:

Firaministan Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine, ya yi Allah wadai da matakin da kasar Benin ta ɗauka na hana ƙasarsa fitar da manta.

Ali Lamine Zeine ya ce matakin ya saɓa wa yarjejeniyar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Matsalar da ke tsakanin ƙasashen biyu, na nufin cewa Nijar da abokiyar kasuwancinta na China ba za su iya fara fitar da ɗanyen man da ƙasar ta fara hakowa ba, wanda kuma hakan zai ba ta damar magance wasu matsalolin na tattalin arziki da take fuskanta.

Cikin wani taron manema labarai da ya gabatar a Yamai babban birnin ƙasar, firaministan ya zargi Benin da bai wa ‘yan ta’adda mafaka da nufin wargaza Nijar.

Hukumomin Benin sun musanta zarge-zargen.

Ko a makon da ya gabata ma ƙasar ta rufe tashar ruwanta da Nijar a wani mataki na mayar da martani kan ƙin buɗe kan iyakar ƙasar da Nijar ɗin ta yi domin shigar da kayyaki daga Benin.

To sai dai Firaministan na Nijar ya ce ƙasarsa ta ƙi buɗe kan iyakar ne saboda dalilai na tsaro.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...