Saurari premier Radio
30.7 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiFara yakin neman zabe:INEC ta ja kunnen jam'iyyu

Fara yakin neman zabe:INEC ta ja kunnen jam’iyyu

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Yayin da ya rage awannin 24 a fara yakin neman zabe a kasar nan, hukumar INEC ta ja kunnen jam’iyyu da su gudanar da yakin neman zaben cikin lumana da kwanciyar Hankali.

 

Hukumar ta ce dukkanin jam’iyyu su mayar da Hankali wajen yin aiki da ka’idojin da kundin tsarin mulkin kasa da dokar zabe da kuma dokar Yan sandan ta tanada domin gudanar da yakin neman zabensu cikin koshin lafiya.

 

Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan Kiran yayin bude taron karawa juma sani na wuni biyu Kan shirye-shiryem tunkarar zaben 2023 a jihar Lagos.

 

Yayin taron shugaban hukumar ya kuma bayyana abubuwan da ya kamata jam’iyyu su yi da wanda za su gujewa.

 

Ya ce kundin tsarin mulkin kasa da dokokin zabe a bayyane suke, a don haka ya kamata jam’iyyu su san me ya kamata su yi da wanda bai kamata ba.

 

Ya kara da cewa ba za a yarda da yin amfani da wakokin siyasa da ke cike da zambo ko zagi ba, musamman wanda zai taba addini da kabila, ko kuma ya taba muru’ar wani.

 

Ya kuma ja hankalin kafafen yada labarai da kada su nuna son rai wajen rohotanninsu, a cewarsa kada su yarda wani dan siyasa ya siyesu.

 

 

Latest stories

Related stories