33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiAPC ta dage lokacin fara yakin neman zaben ta

APC ta dage lokacin fara yakin neman zaben ta

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Jam’iyyar APC ta janye shirinta na fara yakin neman zaben da ta tsara farawa ranar Talatar nan.

 

Darkatan yakin neman zaben gwamnan Filato Simon Lalong ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

 

Ya ce an daga fara yakin neman zaben ne saboda a samu karbar wadanda suke ta nuna sha’awar su shiga a yi tafiya tare da su.

Lalong ya ce nan gaba kadan za a Sanya wata sabuwar ranar da za a fara yakin neman zaben.

 

“Idan za ku tuna mun tsara za muyi tattakin zaman lafiya da gudanar da addu’o’i a ranar Laraba 38 ga Satumba domin kaddamar da yakin neman zaben mu.

 

“Haka kuma mun ce dukkanin mambonin yakin neman zabenmu su hadu a shalkwatar jam’iyyar domin karbar takardun kama aikinsu.

 

“Sai dai saboda Kara adadin wadanda za su yi yakin neman zaben, munyi shawarar daga lokacin fara yakin neman zaben domin tabbatar da kowa ya shigo don ayi tafiyar tare.” A cewarsa.

 

Latest stories