Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa sabon matakin sayar da man fetur a farashi na ainihin kuɗin da aka kashe wajen samo shi, ba yana nufin gwamnati ta dawo da tallafin man fetur ba ne.
Gwamnatin ta ce kamfanin man fetur na ƙasa, NNPCL, zai rage ribar da yake ƙarawa kan farashin sayar da man fetur na tsawon kwanaki 30, domin rage wa ’yan Najeriya nauyin tashin farashin mai a kasuwannin duniya.
A cewar ministan kuɗi, Taiwo Oyedele, za’a ba masu zirga-zirgar jama’a fifiko a wannan shiri, yayin da ake sa ran matakin zai taimaka wajen rage matsin lamba kan kuɗin sufuri.
Gwamnatin ta kuma ce tana tattaunawa kan kayyade kuɗin da za’a riƙa sayar da man fetur daga matatun mai ko wajen shigo da shi, a kan naira 1,350 kan kowace lita, domin saukaka farashi.
Sai dai matakin ya zo ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke fuskantar tsadar man fetur da tsadar rayuwa, lamarin da ya sa wasu ’yan siyasa ke bayyana shakku kan ko rangwamen na kwanaki 30 zai samar da sauƙi mai ɗorewa.
