CITAD ta raba tufafi da kayan karatu ga Yara 100 na makarantar firamaren Fulani ta Nomadic dake Kamanda Dan Soshiya a karamar hukumar Kiru a jihar Kano.
Wannan wani bangare ne na bunkasa fanin ilimin Yara da cibiyar ke yi a sassan kasar nan.
Da yake bayyana makasudin ziyarar, Babbban daraktan cibiyar CITAD, Dakta Yunusa Zakari Ya’u yace damuwa da halin da ilimin yara ke ciki musamman Fulani dake karkara ne ya sanya bujuro da wannan shiri.
YZ Ya’u ya kuma yi tsokaci kan yadda karancin ilimi ke sanya aikata laifukan ta’addanci tare da kira ga mahukunta da shigo don taimakawa fannin ilimin da kawo karshen matsalar.
Malam Nasiru Ibrahim Dangora shi ne Headmastan makarantar yace a kalla suna da yara kusan dari uku, sai dai har yanzu suna fama da wasu matsalolin gudanarwa.
Da yake tsokaci yayin taron, Dagacin Dangora Yusuf Harisu da ya wakilci Hakimin Kiru, ya bukaci iyayen yara su tabbatar sun tura yara makaranta tare da bibiyar su.
Malam Muhammad daya ne daga cikin iyayen yaran da ya’yansa suka fi yawa a makarantar, cikin harshen fillanci ya bayyana muhimmacin tura yara irin wadannan makarantu don samun ingattaccen Ilimi.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin ilimin makarantar firamaren Fulani ta Nomadic na yankin Kiru wanda daga bisani CITAD ta tabbatr da cigaba da bibiyar Irn wadannan makarantu tare da tallafa musu iya karfinta.
