Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Danagundi, ya ce babu wata yarjejeniya ta siyasa da za ta iya cire Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ko iyalan Bayero daga karagar mulkin Kano.
Sarkin Dawakin ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya ce shari’ar tana gaban Kotun Koli, kuma hukuncin kotu kaɗai ne zai warware rikicin, ba tattaunawar siyasa ba.
Ya ƙaryata batun da ke cewa rikicin zai iya warwarewa ta hanyar sulhu bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya daidaita da jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne.
Ya jaddada cewa marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, ya yi sarauta fiye da shekaru 50 ba tare da aikata wani laifi ba, don haka a ganinsa ɗansa, Aminu Ado Bayero, shi ne ya dace ya gaje shi, ba wani daga wani iyali ba.
Danagundi ya ce shari’ar da ya kai kotu ba ta shafi cire sarki kai tsaye ba, illa dai ta shafi rashin bin ƙa’ida da tsarin doka wajen soke dokar masarautar Kano.
Ya kara da cewa soke dokar ya shafe shi kai tsaye ta hanyar cire shi daga mukaminsa, lamarin da ya ce ya tauye masa haƙƙoƙinsa na kundin tsarin mulki, wanda ya sa ya garzaya kotu.
A ƙarshe, Danagundi ya bayyana fatan cewa Kotun Koli za ta yi adalci, yana kuma kira ga kowa da kowa da ya jira hukuncin kotun cikin haƙuri.
