Gwamnatin Kano ta bada kyautar Riyal 200 ga kowane maniyyaci da ya fito daga jihar, da nufin tallafa musu ta yadda zasu ji dadin gudanar da aikin hajjin su na bana a kasar Saudiyya cikin nutsuwa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi a wajen horaswa ta musamman a aikace ga maniyyatan Kano yadda ake gudanar da ibadun aikin hajji gabanin tafiyar su kasa mai tsarki.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Murtala Sule Garo, ya bukaci maniyyatan da su mutunta dokokin kasar Saudiyya yayin gudanar da ibadar ta su, inda ya ce gwamnati ta dauki matakai masu kyau domin tabbatar da jin daɗi da walwalar maniyyatan Kano a lokacin aikin Hajjin.
Shi ma da yake jawabi, shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta Kano Abubakar Ibrahim Matawalle, ya ce an shirya horaswar ne domin baiwa maniyyatan cikakken ilimin yadda ake gudanar da aikin Hajji a aikace, inda ya ce tuni hukumar ta tura malamai da jami’ai kwararru domin wayar da kan maniyyata muhimmancin biyayya ga dokoki da hakuri yayin gudanar da aikin Hajjin.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa horaswar ta gudana ne a sansanin alhazai na Kano, inda aka nunawa mahalartansa yadda ake daura Ihrami, yin dawafi a ka’aba, gudanar da sa’ayi tsakanin safa da marwa, tsayuwar arfa, kwana a Muzdalifa da Mina tare da jifan jamrori bisa koyarwar addinin Musulunci.
