Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano, PHIMA, ta yi barazanar rufe duk wani asibiti ko cibiyar lafiya mai zaman kanta da ta gaza gabatar da bayanan marasa lafiya na tsawon watanni shida.
Babbar Daraktar Hukumar, Khadija Hussain Sa’id, ta bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan masu asibitoci masu zaman kansu da daraktocin kiwon lafiya kan muhimmancin tattarawa, adanawa da amfani da bayanan lafiya.
Ta ce gwamnati na bukatar sahihan bayanai domin tsara manufofin kiwon lafiya, inganta ayyukan jinya da kuma yanke ingantattun shawarwari.
Khadija ta jaddada cewa wajibi ne dukkan cibiyoyin lafiya masu zaman kansu su rika gabatar da bayanan marasa lafiya akai-akai.
A nasa bangaren, jami’in kula da tattarawa da tantance bayanan lafiya, Muhammad Sidi Abdullahi, ya ce shigar da cikakkun bayanan marasa lafiya cikin tsarin gwamnati na taimakawa wajen gano yawaitar cututtuka da kuma tsara hanyoyin magance su.
A yayin taron, an bayyana cewa daga cikin sama da cibiyoyin lafiya 600 da ke jihar Kano, cibiyoyi 239 ne kawai ke gabatar da bayanai akai-akai kamar yadda ake bukata.
Gwamnatin jihar ta ƙara jan hankalin masu asibitoci da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu da su kiyaye tsarin bayar da bayanai domin kauce wa matakin rufe cibiyoyinsu.
